ADC Ce Jam’iyya Mai Kyakkyawar Makoma a Najeriya – Bashir Umar

Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a ƙaramar hukumar Zaria ta Jihar Kaduna, Hon. Bashir Umar, ya yi kira ga mambobi da magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da bai wa jam’iyyar haɗin kai da goyon baya domin ƙarfafa ta a matakai daban-daban.

Hon. Bashir ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a Zaria, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin mambobin jam’iyyar domin tabbatar da cigaban ta da kuma samun nasara a harkokin siyasa a nan gaba.

Ya kuma yi kira ga al’umma, musamman masu cancantar shiga siyasa, da su fito su yi rajista da jam’iyyar ADC, yana mai cewa faɗaɗa yawan mambobin jam’iyyar na daga cikin matakan da za su taimaka wajen gina jam’iyya mai ƙarfi da tasiri a ƙasar nan.

Dangane da batun da ya shafi tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da hukumomin ICPC da EFCC ke yi, Hon. Bashir ya ce ya kamata a gudanar da lamarin cikin adalci da kuma bin doka da oda.

A cewarsa, yana da muhimmanci hukumomin da ke da alhakin tabbatar da gaskiya su yi aikinsu bisa ƙa’ida domin ci gaba da samun amincewar jama’a a kan tsarin shari’a da shugabanci a ƙasar.

Hon. Bashir Umar ya kuma yaba da jagorancin shuwagabannin jam’iyyar ADC a matakin ƙananan hukumomi, jiha da kuma na ƙasa, yana mai cewa suna kokarin gina jam’iyya mai ƙarfi wadda za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin da ke fuskantar ‘yan Najeriya.

A ƙarshe, ya yi kira ga al’umma, musamman a wannan lokaci na azumin watan Ramadan, da su ci gaba da yin addu’a domin samun nasarar jam’iyyar ADC da kuma zaman lafiya da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Comments

Popular posts from this blog

Pathway to Purpose Initiative Strengthens Community Outreach with NDLEA Partnership, Hospital Support in Zaria

Pathways to Choice Project Targets Improved Literacy for Girls in Kaduna Communities

KANO REJOICES AS GOVERNOR ABBA YUSUF NOMINATES GARO FOR DEPUTY GOVERNOR