Zargin 419: Kotu Ta Ci Gaba da Shari’ar Sanata Abdu Kwari a Zariya
An ci gaba da sauraren shari’a a yau, 30 ga Maris, 2026, a Babbar Kotun Shari’a ta Dogarawa da ke Zariya, Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Justice Yakubu Badamasi, a shari’ar da ake yi kan zargin zamba da haɗa bakin makarkashiya da ta shafi Abdu Kwari, Hajiya Amina Dalhatu Akilu da Shehu Abdu Kwari. Shari’ar ta samo asali ne daga ƙorafin da wani ɗan kasuwa mazaunin Zariya, Ahmed Muhammad Gusau, ya shigar, inda ya zargi waɗanda ake ƙara da yaudararsa wajen musayar kadarori. A cewarsa, ya bayar da gidansa da ke lamba 17, titin Sale Annur, Kabama Layout, Sabon Gari, Zariya, wanda darajarsa ta kai naira miliyan 60, domin a musanya da wani fili da ke lamba 5, titin Abubakar Mustapha Road, Kabama Layout, wanda ake zargin mallakin Sanata Abdu Kwari ne, mai darajar naira miliyan 20. Ya ƙara da cewa an sanar da shi cewa Sanatan ba ya sayar da fili sai dai yana yin musayar kadarori ne kawai, wanda hakan ya sa ya amince da yarjejeniyar. Bayan kammala takardar mallaka (Deed of Assign...