Tasirin Zarge-zargen Cin Hanci Kan Makomar Siyasar Bauchi
Daga Usman Dahiru, Bauchi. Daga yadda rahotanni da zarge-zargen da ke alaƙa da rashin gaskiya ke ci gaba da fitowa dangane da tsohon jami’in NAPIMS, Bala Wunti, wanda ake alakantawa da zargin cin hanci da rashawa a lokacin da yake ofis, al’ummar Jihar Bauchi na ƙara fahimtar irin siyasar da aka dade ana yi a kansu: siyasa wadda ke amfani da mulki a matsayin kariya daga bincike, kuma a matsayin hanyar kare muradu na kai. Zarge-zargen da ke nuna yunƙurin amfani da jam’iyyun siyasa da kusanci da masu iko domin kauce wa yin hisabi ba abin mamaki ba ne ga masu bibiyar siyasar Bauchi. Tun da daɗewa akwai alamun cewa wasu mutane na ganin siyasa a matsayin mafaka ta kariya maimakon dama ta yi wa jama’a hidima. Abin baƙin ciki ne matuƙa cewa tattaunawa kan burin siyasa da rabon mukamai na faruwa a daidai lokacin da talakawa ke fama da fatara, rashin tsaro, rashin aikin yi da tsananin wahalar rayuwa. Maimakon mayar da hankali kan yadda za a inganta rayuwar jama’a, wasu ‘yan siya...