Yusuf Maitama Tuggar: Daga Diflomasiyya Zuwa Fatan Gina Sabuwar Jihar Bauchi
Daga Muazu Abubakar Albarkawa, Kaduna Batun zaɓen gwamnan shekarar 2027 a Jihar Bauchi ta dauki sabon salo mai jan hankali da ban sha'awa sakamakon fitowar tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, a matsayin dan takara tare da dimbin kwarewa a harkokin diflomasiyya, gogewa a majalisa, da kusanci da al’umma, takararsa na zama wata alama ta fata, sabuwar rayuwa, da shugabanci mai manufa. An haifi Tuggar a ranar 12 ga Maris, 1967, cikin gida mai alaka da siyasa a Gamawa, inda tun daga farko al’amuran jagoranci suka bayyana a rayuwarsa. Mahaifinsa, Abubakar Tuggar, ya kasance fitaccen dan siyasa a lokacin Jamhuriya ta Farko, wanda ya kafa tubalin hidimar jama’a da ya shafi rayuwar Tuggar. Tun yana karami, ya taso cikin darussan shugabanci, nauyi, da kishin kasa wadanda suka zama ginshikin rayuwarsa. A bangaren ilimi, Tuggar ya yi fice a matsayin mutum mai zurfin tunani da hangen nesa na duniya. Ya yi karatun hulda da kasashen waje, sannan ya kara ilimi a Jami’a...