El-Rufai na zubar da jini ta hanci a yayin da yake tsare a hannun ICPC, in ji mai magana da yawunsa


Mai taimaka wa Nasir el-Rufai kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce tsohon gwamnan na zubar jini ta hanci cikin dare yayin da yake tsare a hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Ya ce an hana matar el-Rufai kai masa abinci kai tsaye, kuma lauyoyinsa ba su ga umarnin kotu da ya halatta tsare shi fiye da sa’o’i 48 ba tare da tuhuma ba.

EFCC da ICPC na bincikensa kan zargin almundahanar kuɗi a lokacin mulkinsa.

 A halin yanzu, ana sa ran kotu za ta saurari ƙarar kare haƙƙoƙinsa, yayin da kuma ake shirin gurfanar da shi kan wasu zarge-zarge a wannan makon.

Comments

Popular posts from this blog

Pathway to Purpose Initiative Strengthens Community Outreach with NDLEA Partnership, Hospital Support in Zaria

Pathways to Choice Project Targets Improved Literacy for Girls in Kaduna Communities

KANO REJOICES AS GOVERNOR ABBA YUSUF NOMINATES GARO FOR DEPUTY GOVERNOR