An sake samun tashin gobara a kasuwar Dakata ta Jihar Kano
![]() |
A safiyar yau gobara ta sake tashi a wata kasuwa da ke unguwar Dakata a Kano, inda ta cinye shaguna fiye da 50 da injinan sarrafa man girki da robobi.
Wannan lamari na zuwa ne 'yan kwanaki bayan gobarar da ta tashi a kasuwar Singa da ke jihar, wadda ta lalata shaguna da dukiyoyi.

Comments
Post a Comment